Mazauna bakin gabar teku a birnin Rio de Janeiro, sun wayi gari da abun al’ajabi, na mutuwar miliyoyin kifaye a cikin kogin Rodrigo de Freitas. Masana hallitun ruwa sun daura alhakin hakan akan matsanancin zafi da aka samu.
Hakan nada alaka da dumamar yanayi da ake samu a fadin duniya, gurbatar yanayi ba kawai yana shafar rayuwar bil’adama ne kawaiba, harma da sauran hallitu, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar wadannan kifayen a cewar masanan.
A shekarar 2016 lokacin wasannin duniya da aka gabatar a kasar ta Brazil, anyi amfani da kogin wajen gudanar da wasu wasanni, ministan muhallin kasar ya fitar da wata sanarwa da tace, tun a ranar Alhamis suka fahimci iskar da Tekun ke fitarwa ta gurbata.
A cewar wani masani Mario Moscatelli, yace yakan ziyarci tekun duk shekara, wanda yake da yakinin cewar dumamar yanayi ke haddasa mutuwar dabbobin ruwa da ma na doron kasa.
Facebook Forum