Dubban Musulmi a kasashe dabam dabam yi zanga zangar nuna bacin ransu dangane da batuncin da wata Mujallar kasar Faransa mai suna Charlie Hebdo ta yiwa Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabata a gare shi. Wasu zanga zangar da aka yi sun buge da zama tarzoma.
Domin a jamhuriyar Niger, an kashe kimamin mutane hudu jiya Juma'a a birnin Zinder dake kudancin kasar, inda masu zanga zanga suka bankawa cibiyar al'adu ta kasar Faransa da wasu coci coci wuta. Jami'ai sunce wani dan sanda yana daya daga cikin wadanda aka kashe.
Haka kuma anyi mumunar zanga zanga a birnin Karachi kasar Pakistan inda daruruwan masu zanga zanga suka yi arangama da yan sanda. An bada rahoton cewa wani dan jarida mai daukan hoto wa kamfanin dilancin labarun Faransa yana daya daga cikin mutane ukun da suka ji rauni.
An kuma yi zanga zanga a wasu biranen kasar Pakistan, ciki harda birnin Islamabad da Lahore.
A kasar Algeria, yan sanda sunyi arangama da masu zanga zanga wadanda suka rika jifa da duwatsu da kuma kwalabe. Tunda farko daruruwan mutne ne suka yi jerin gwano cikin lumana a titunan baban birnin kasar dauke da katin da aka rubuta cewa Nine Mohammad.
An kuma yi jerin gwano cikin lumana a manyan biranen kasashen Mali da Senegal da kuma Mauritana.
Sa'anan an yi jerin gwano a birnin Amman na kasar Jordan da kuma birnin Istanbul kasar Turkiya.