Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Jama'a Suna Zanga Zanga a Washington


Dubban jama'a suka hallara domin zanga zangar neman sauyi kan yadda ake binciken 'Yansanda
Dubban jama'a suka hallara domin zanga zangar neman sauyi kan yadda ake binciken 'Yansanda

Iyalan wasu bakar fata suna cikin wadanda suke zanga zangar rashin adalci daga jami'an tsaro.

Dubban jama'a ne suke gangami a anan Washington yau Asabar, domin zanga zanga kan kisan bakar fata da 'Yansanda suke yi, suna neman a aiwatar da sauye sauye.

Iyalan Micael Brown da Eric Garner, da Tamir Rice, da Trayvon Martin, wadanda dukkansu masu zanga zangar suka kira wadanda aka halaka dalilin wariyar launin fata, a zanga zangar da masu macin suka kira ta neman a nuna adalci ga kowa.

Anyi gangamin da macin ne kusa da harabar majalisar dokokin Amurka, a zaman wani bangare na jerin zanga-zangogi a fadin kasar a yau Asabar, da wata kungiya da ake kira Feguson Action da turanci ta shirya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG