Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: YULI 06 2017, Yadda Batun Raba Kasa Zai Shafi Rayuwar Iyali


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana takaici kan matakan da wadansu ‘yan tsirarru a kasar suke dauka dake barazana ga hadin kan kasa.

Wannan ya biyo bayan tada kayar baya da wadansu matasa 'yan Kabilar Igbo suka yi suna ikirarin shirin ballewa daga kasar, yayinda wadansu matasa a arewacin kasar suka maida martani tare da ba ‘yan kabilar Igbo wa’adin watanni uku su tattara kwansu da kwarkwatarsu su fice daga arewacin kasar.

Kasancewar wannan filin na Domin Iyali kamar hatsin bara ne a duk abinda ya shafi iyali, yana da ruwa da tsaki a duk wani abinda zai iya kasancewa kadandaren bakin tulu a ci gaban iyali.

Kawo yanzu dai shugabanni da dama sun sa baki sun yayyafawa wannan wuta ruwa, abinda ake gani zai kai ga samun masalaha idan aka dace, sai dai lafazin wadansu matasa har ma da wadansu da suka manyanta yasa shirin domin iyali a nashi gudummuwa, yaga ya kamata mu tattauna alakar wannan batu da makomar iyalanmu, kasancewa muna tarayyar nan shekara da shekaru tsakanin kabilun kasar nan.

A cimma wannan burin shirin ya yi zama na musamman a birnin tarayya Abuja da kuma Kano, da wadansu daga cikin manyan kabilun kasar nan, wadanda kowanne dayansu aka haifeshi ya kuma girma har ya kai ga manyanta a wani yanki ko kuma jiha daban da jiharsa ta asali. Zamu fara da jihar Kano, tumbin giwa inda wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya yi wani zaman tattaunawa na musamman da Alhaji Abdulrazak Tanimawo wani dattijo dan kabilar Yarbawa da aka haifa a Kano sama da shekaru tamanin da suka shige, da kuma Cif Ifenyi Anya mutumin Nnewi a jihar Anambra wanda shima aka haifeshi a jihar Kano shekaru sittin da daya da suka shige, da kuma Mallam Ibrahim Maidawa Fagge wanda dan asalin jihar Borno ne, amma an haifeshi a jihar Kano shekaru hamsin da daya da suka shige.

Dukansu sun bayyana irin gwaggwarmayar da suka sha, a rayuwa da illar bangaranci, da kuma bukatar zaman lafiya da ci gaban hadin kan kasa.

Ka Saurari Cikakken Shirin Domin Karin Bayani A hirar da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari Ya Hada Mana.

Domin Iyali-Hadin Kan Kasa-10'15
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:15 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG