Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI:Tattaunawa Kan Tarbiyar 'Ya'ya- Kashi Na Daya -Maris 18, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Wani abu da yake da muhimmanci ga yadda al'umma ke kallon iyali shi ne tarbiyar 'ya'ya. Abinda akan ci gaba da ambato musamman tsakanin surukai da ma'aurata. Sau da dama akan danganta halayar matasa da irin tarbiyar da suka samu ko kuma akasin haka.

Ganin yadda wannan batu yake ci gaba da daukar hankali ya sa Shirin Domin Iyali sake nazarin wannan lamari, bayanda kwanan nan, wani magidanci ya nemi kotu ta raba aurensu da matarsa da ya ce ta kwasa mashi mari sabili da bata amince da yadda yake tarbiyantar da dansu ba.

Shirin ya kuma gayyaci masu ruwa da tsaki, iyaye maza da mata kuma 'yan gwaggwarmaya domin musayar miyau kan Tarbiyar 'ya'ya.

Saurari tattaunawar da Baraka Bashir ta jagoranta:

DOMIN IYALI:Tattaunawa Kan Tarbiyar 'Ya'ya- Kashi Na Daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:22 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG