Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI:Tattaunawa Kan Matsalar Tsaro A Makarantun Najeriya-Kashi Na Daya-Janairu 07, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Babban kalubale da iyali ke fuskanta a Najeriya banda koma bayan tattalin arziki da ya shafi kowanne bangaren rayuwa, shi ne matsalar tsaro da kwarru su ka yi harsashen cewa, zai iya haddasa karancin abinci da mai yiwuwa ya kai ga yunwa a wadansu sassan Najeriya, matsalar da yanzu haka take barazana ga harkokin ilimi musamman a arewacin kasar da ake ci gaba da fuskantar garkuwa da daliban makaranta.

Ta haka shirin Domin Iyali ya gayyaci masu ruwa da tsaki domin yin nazarin wannan matsala da kuma neman hanyar shawo kanta, da nufin ba manyan gobe damar samun ilimi da zai taimaki rayuwarsu, ya inganta matsayin iyali da kuma ci gaban kasa.

Saurari tattaunawar da Baraka Bashir ta jagoranta:

Tattaunawa Kan Matsalar Tsaro A Makarantun Najeriya-Kashi Na Daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:46 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG