Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Nazari Kan Tsarin Almajiranci A Jihar Zamfara-Kashi Na Daya-Satumba, 12, 2024


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Shirin Domin Iyali na wannan karon ya tattauna a kan batun kai yara kanana da ba su mallaki hankalinsu ba almajiranci da sunan makaranta.

Domin nazarin lamarin, shirin ya tattauna da Shugaban Majalisar Tuntuba ta Malamai a Jihar Zamfara, Sheikh Ahmad Bin Umar Kanoma, da Hassan 'Yan Buhu (Magidanci) kuma Shugaban Kungiyar Mabuga waya ta jihar Zamfara, da kuma Nafisa Sheikh Murtadha Zawiyya.

Saurari cikakken shirin:

09_12_24_ ZAMFARA ALMAJIRI SYSTEM PT1.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:08 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG