Idan kuna tare damu makon da ya gabata muka fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan al’amuran da suka shafi zamantakewar iyali da nufin ganin irin darasin da za a koya daga abinda ya faru da matashiyar da aka yiwa aure tana ‘yar shekaru13 da ya kai ga rasa rai. A yau shirin ya bayyana wadansu daga cikin dalilan da ke kawo sabani tsakanin iyali.
Bakin da muka gayyata a shirin sune, Barista Badiha Abdullahi Mu’az, daya daga cikin lauyoyin da suke kai komo musamman kan al’amuran da suka shafi iyali, da Dr Musa Abdullahi Sufi na gidauniyar A.A Gwarzo dake ayyukan lafiya da jinkan al’umma, sai kuma Mallam Mustapha Mohammed Dandume wanda ke koyarwa kan al’amuran da suka shafi rayuwar Musulmi.
Saurari tattaunawar da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta: