Ga wadanda suka jima suna sauraron shirin Domin Iyali, sun sha jin shirin na haska fitila kan matsalar fyade da ake fama da ita a Najeriya. Sai dai, kawo yanzu, hakar shirin bata cimma ruwa ba domin ganin yadda lamarin yake kara ta’azzara musamman a wannan lokacin da aka hana zirga zirga, da ya kai ga mata a sassa dabam dabam na kasar suka shiga zanga zangar kira ga hukumomi da shugabannin al’umma su dauki mataki.
Ta haka, shirin Domin Iyali ya gayyaci ‘yan fafatuka mata da nufin neman hanyar dakile wannan mummunar dabi’a.
Wadanda muka gayyato sun hada da kwamishinar ma’aikatar harkokin mata ta jihar Nassarawa Hajiya Halima jabiru, da Saudatu Mahdi shugabar kungiyar kare hakkokin mata da kananan yara WRAPA, da Hajiya Safiya Adamu, daya daga cikin shugabannin kungiyar dake hankoron kare hakkokin kananan yara da ake kira Tallafi Najeriya, sai kuma Aisha Buba kwararriya a fannin sanin halayyar dan adam.
Saurari kashin farko na tattaunawar da wakiliyar Sashen Hausa, Shamshiya Hamza ta jagoranta.
Facebook Forum