Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Kulle Matashi a Kano, Kashi Na Uku-Satumba, 03, 2020


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Likitoci a asibitin kwararru na Murtala Mohammed dake Kano sunce matashin nan Ahmed Aminu da ya fuskanci ukubar dauri a wurin mahaifin sa na tsawon shekaru 7 ya kama hanyar komawa hayyacinsa. Yayinda gwamnatin Jihar Kano ta bayyana fara daukar matakan da suka dace akan mahaifin.

Shirin Domin Iyali ya ziyarci matashin a gadon asibiti inda ake yi mashi da sauran yaran da iyayensu suka kulle su jinya.

Saurari bayanin da ya yi wa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari, da kuma bayani kan matakan da gwamnatin jihar Kano ta fara dauka dangane da wannan lamari

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Kulle Matashi a Kano, Kashi Na Uku-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:19 0:00


.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG