Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Sifaniya Spanish Football Federation's, a turance ta dakatar da dan wasan gaba na Atletico Madrid Diego Costa, daga buga wasanni har guda takwas, bayan haka kuma an ci shi taran bisa samun sa da laifin cin zarafin alkalin wasa.
An baiwa Diego Costa jan kati a wasan hamayya na gasar La Liga da su kayi da Barcelona wace ta doke Atletico da ci 2-0 a Camp Nou ranar Asabar da ta gabata.
Alkalin wasa Jesus Gil Manzano ya rubuta, cikin bayanansa bayan da aka tashi daga wasan, inda ya ce Diego Costa ya ci mutuncin mahaifiyarsa sai dai dan wasan na kasar Spain ya musanta wannan zargin da ake masa.
Duk da kin amincewa da Costa yayi na tuhumarsa hukumar kwallon kafar Spaniya ta ce ta dakatar da dashi wasanni hudu sabo da zagin mahaifiyar alkalin wasan da yayi, har ila yau ta kara haramta masa wasu wasanni hudu sakamakon rike alkalin gam da ya yi.
Wannan na nufin Costa ba zai buga wa Atletico sauran wasanni bakwai da suka rage a gasar La Liga na Spain ba, bayan haka kuma akwai wasa guda daya a kakar badi wanda itama ba zai buga ba saboda hukuncin da aka masa tare da biyan tara ga kungiyar ta Atletico Madarid.
Sai dai tuni kungiyar tasa ta daukaka kara akan wannan hukunci da take ganin ya yi tsanani.
Facebook Forum