David Moyes, ya koma cigaba da horas da 'yan kungiyar kwallon kafa ta West Ham, bayan da ta sallami Manuel Pellegrini, a ranar Asabar da ta gabata, biyo bayan kashi da ta sha a hannun Leicester city a gida da ci 2-1, cikin gasar firimiya lig na bana.
Moyes ya cimma yarjejeniya da kungiyar ta West Ham, inda zai ja ragamar ta na tsawon watanni sha takwas kawai, domin farfado da darajar kungiyar a idon duniya.
Manuel Pellegrini, wanda kungiyar ta sallama shi, ma watanni 18 ya yi ya na jan ragamar kungiyar.
Bayan haka kuma shi ne mai horas da 'yan wasa na shida da aka sallama a al'amura masu alaka da gasar ta Firimiya lig na kasar Ingila a kakar wasan bana cikin makonni ashirin da farawa.
West Ham dai tana matsayi na 19 a tebur mako na 20 a firimiyar bana da maki 19.
Facebook Forum