Shugaban Amurka Barack Obama ya tabbatar da mutuwar wani ba-Amurke Abdul-Rahman Kassig damayakan Kungiyar Daular Islama suka kasha. Shi dai yana aikin agaji ne. Shugan yace abun da Daular Islama tayi abu ne da bashi da Imani.
A wani jawabinsa ga 'yan jaridar da ke tare da shi cikin jirgin saman 'Air Force One,' Mr Obama ya yi addu'a da kuma ta'aziyya ga iyaye da kuma 'yan'uwan Kassig. Ya zargi kungiyar ta ISIS da marmarin hallaka wadanda ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da Musulmi, kuma sun himmatu ga yada mutuwa da barna.
Shugaba Obama na kan hanyarsa ce ta dawowa gida daga taron G20 da aka yi a kasar Australia.
Tabbacin mutuwar Kassig din ya biyo bayan nazarin wani faifan bidiyon da kungiyar ta Daular Islama ta fitar a jiya Lahadi, mai nuna hotunan da aka ce na wasu sojojin Syria ne da masu tsattsauran ra'ayin ke datse wa kawuna, wanda daga karshe kuma ke nuna wani dan bindiga mai ikirarin ya hallaka ba-Amurken.
Faifan bidiyon bai nuna yadda aka datse kansa ba.