Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dauko Sojojin Haya da Gwamnati ke kokarin yi Bai Daceba


A woman walks down stairs advertising a Vincent van Gogh exhibition outside Albertina museum in Vienna.
A woman walks down stairs advertising a Vincent van Gogh exhibition outside Albertina museum in Vienna.

Wasu alamu da suka nuna cewar gwamnatin tarayyar Najeriya, na dauko sojojin haya don yaki da ‘yan ta’addan kungiyar boko haram, amma gwamnati ta musanta wannan maganar.

Ta bakin wasu ‘yan Najeriya kuma masu sharhi a harkar tsaro, na ganin wannan wani abu ne da bai kama taba. A ganin wani tsohon jami’in tsaro, kuma dan gwagwarmayar ‘yanci a Najeriya, Barista Solomon Dalong, yana ganin wannan babban sakaci ne a bangaren gwamnati.

Don wannan babban koma bayane, ace wai gwamnati tana dauko sojojin haya, sabo da kowa yasan karfin sojojin Najeriya a duniya, sai yanzu kuma a ga cewar su ke dauko sojojin wasu kasashe, to a gaskiya wannan bai yi dai dai da kundin tsarin mulkin Najjeriya ba.

Shi kuma Dr. Bawa Abdullahi Wase, naganin wannan ya nuna halin tabarbarewar Nageriya Kenan a idon duniya, wannan zai nuna cewar kasar ta gaza kuma wasu zasu samu damar yin wasu abu don yakar kasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG