Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daukar Mataki Da Wuri Na Kauda Yoyon Fitsari


Wasu Majinyata
Wasu Majinyata

Malama A’isha Hassan, shugabar wata kungiya mai zaman kanta, Forward Nigeria, wadda ke kula da mata masu cutar yoyon fitsari, ta ce muddun aka ce za a yi ma masu yoyon fitsari aiki cikin watanni biyu, da an bude rajista ana iya samun mutane sama da 50.

Wakiliyarmu Baraka Bashir ta ruwaito Malama A’isha na cewa duk da ya ke akwai wadanda sukan zo asibiti ne don a cigaba da masu aikin ko kuma a sake masu wani aikin saboda dalilai dabandaban, sabbin kamuwa da cutar na da yawa sosai. Alal misali, cikin mata hamsin da su kan zo a masu aikin, akan sami mata 20 tsoffin kamuwa, 30 sabbin kamuwa. Ta ce wasu idan an masu aiki ba su samin cikakken lafiya sai an masu sau biyu ko ma sau uku. Wasu ma har likitoci kan ce masu saidai su hakura hakanan musamman idan wuraren da su kan dinka din su ka zama kamar jijiya. To amma wani lokacin idan su ka rinka cin abinci mai gina jigi, wurin na iya sake toho har a iya masu aikin.

Malama A’isha Hassan ta ce ya kamata bangarorin da ba na gwamnati ba su shigo cikin wannan al’amarin sosai saboda bai kamata a bar ma gwamnati ita kadai ta ji da wannan batu ba. Ta ce ya kamata jama’a su rinka zuwa wuraren da masu matsalar yoyin bitsarin su ke don su rinka tausaya ma su. Ta kuma yi kira ga Malamai da su rinka yin wa’azi ma maza da kuma iyaye a guji saboda wani lokacin abin kan faru ne sanadiyyar yanka sassan farjin mace da wanzamai kan yi. Ta ce babban magani shi ne zuwa asibiti.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG