Wani babban jami’in aikin jinya a nan Amurka yace dan kasar Liberiyan nan da ake jinya a wani asibitin birnin Dallas a jihar Texas yana kwance rai kwakwai-mutu-kwakwai.
Dr. Thomas Frieden na cibiyar yaki da cututuka ta Amurka CDC- ya shaidawa shirin talabijin na CNN-State of the Union jiya Lahadi cewa, samun dukan mutanen da Thomas Eric Duncan ya yi hulda da su zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
Yace dalili ke nan da yasa yake da kwarin guiwar cewa, cutar ba zata yadu a Amurka ba. Sai dai yace, hukumomi sun damu matuka da abinda yake faruwa a Afrika ta yamma, daga inda yace cutar zata iya bazuwa zuwa wadansu kasashen duniya muddin ba a shawo kanta ba.
Jikin Duncan ya kara tsananta ranar asabar. An same shi da cutar Ebola kwanaki hudu da suka shige bayan isowarsa Amurka ranar ashirin ga watan Satumba daga Liberia.