Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangantaka da Abokai Nagari Jari ne a Rayuwar Yau


Kujeru
Kujeru

Abokantaka da aboki nagari wani abune me matukar mahimanci da yakamata ace kowane matashi ko matashiya su maida hankali akai.

Kasancewar idan matashi ko matsashiya sunada abokai masu natsuwa to akwai tabbacin cewar dukkansu zasu zamo masu hankali, wannan wani abune da yakamata ace iyaye su maida hankali wajen ganin 'yayansu suna abokantaka da yara da suka fito daga gidan masu tarbiyya.

Yusuf Usman, wani matashine da ya bayyanamuna irin halin da yasamu kanshi, tun yana dan makarantar sakandire, yafara sana’ar koyon aikin kafintanci, wanda wannan aikin yayi sha’awar shine a sanadiyyar wani abokinshi yana koyon wannan aikin. Sai wannan abokin nashi ya samishi wannan ra’ayin kuma bayan ya fara har gashi yanzu yazama maigidan kanshi da yaranshi.

Abun sha’awa an nan shine idan da wannan matashin bai samu aboki na kwarai da ya nuna mishi wannan hanyar ba to da yana iya zama wanda bai san abun da ya dace da shi ba. Duk da haka wannan matashin bai zauna hakaba sai da ya koma don kamala karatunshi na sakandire, saboda yasan mahimanci zama mai ilimi koda kuwa kana da wata sana’a, yakamata ace ko kasuwanci mutun yakeyi to yazama mai ilimi don magance ko wace irin matsala ta fuskantoshi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG