Benjamin Pavard dan wasa mai tsaron baya na tawagar kwallon kafar kasar Faransa, zai koma kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus da cigaba da fafata wasa, ranar 1 ga watan Yulin shekara 2019, daga kulob dinsa na Stuttgart.
Dan wasan yana daya daga cikin 'yan wasan Faransa wanda suka lashe kofin duniya na 2018, da ya gudana a kasar Rasha.
Zai koma kungiyarne kan zunzurutun kudi har Yuro miliyan £35, bisa yarjejeniyar shekara biyar. Dan wasan Pavard mai shekara 22 da haihuwa ya taho Stuttgard daga kungiyar kwallon kafa ta Lille akan kudi Yuro miliyan 11, amatsyin mai tsaron baya.
A wasan da Faransa ta doke Argentina da ci 4-3 cikin gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a shekara ta 2018, Pavard ya jefa kwallaye hudu daga cikin wanda kungiyar ta zura.
Facebook Forum