Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya jefa kwallon sa ta 400, a bangaren gasar La-liga na kasar Spain, Messi ya samu wannan nasarar ne bayan ya jefa kwallo guda a wasan da Barcelona ta lallasa Eibar daci 3-0 cikin wasan mako na 19 a ranar Lahadi da ta gabata, inda Luis Suarez ya zura kwallaye biyu cikin ukun da suka saka.
Wannan kwallon da Messi ya zura tasa ya kara nisa a tarihin cin kwallaye a gasar ta La Liga, tsohon dan wasan Real Madrid ne kawai Cristiano Ronaldo, ya taba cin kwallaye fiye da 300 a wasanni 435, da ya buga a lokacin yana taka leda a kungiyar Real Madrid kafin ya koma Juventus.
Messi ya buga wasanni guda 22 wa kungiyar Barcelona cikin kakar wasan bana 2018/19, ya zurara kwallaye 23, sha 17 daga ciki duk a gasar La Liga ne, kuma shi yafi kowa cin kwallaye a yanzu haka a wasannin mako na 19.
Barcelona dai tana saman teburin da maki 43, banbancin maki biyar tsakaninta da Atletico Madrid wace take ta biyu a teburin La Ligar bana.
Yawan kwallaye da 'yan wasan Barcelona Messi da Suerez suka jefa, sunfi duk yawan kwallayen da Real tasha a bana bangaren gasar La Liga.
Facebook Forum