Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta shaida wa kulob din Inter Milan cewar, dan wasanta Jan Vertonghen, ba na sayarwa bane.
Tun a farkon kakar wasannin bana ne Inter Milan ta nuna sha'awar daukan dan wasan, amma hakarta bata cimma ruwa ba, sai yanzu ta sake sa ran daukar dan wasan a watan Janairu 2020, da zarar an bude saye da sayarwar 'yan wasa, tace zata bashi damar yarjejiniyar shekaru uku.
Vertonghen wanda ya zo kungiyar ta Tottenham tun a shekarar 2012, zai karkare kwantirakinsa ne a karshen kakar wasan bana, inda ake ganin zai koma Inter a matsayin kyauta (Free Agent) a watan Janairu mai zuwa, a kokarinta na inganta masu tsaron bayanta a 2020/21.
Ba shi kadai ne zai bar kungiyar ta Tottenham ba, cikin 'yan wasan da ake ganin zasu bar kulob din sun hada Toby Alderweireld, da kuma Christian Eriksen, wanda manyan kungiyoyi a nahiyar turai suke zawarcensu.
Tottenham dai tana mataki na sha daya ne a teburin Firimiya Lig na bana, wasan mako na 11 bayan da Liverpool ta doketa da kwallo 2-1 ranar Lahadin da ta gabata.
Facebook Forum