Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Najeriya Ya Maida Kudin Tsintuwa, Ya Ki Karbar Tukwici a Japan


Ikenna Nweke, dan Najeriya da ya tsinci kudi a Japan ya kai wa 'yan sanda (Fadar Shugaban Najeriya- Bashir Ahmad)
Ikenna Nweke, dan Najeriya da ya tsinci kudi a Japan ya kai wa 'yan sanda (Fadar Shugaban Najeriya- Bashir Ahmad)

Wani dan Najeriya da ke karatu a Japan ya tsinci wasu "makudan kudade" ya kuma mika su ga 'yan sandan kasar.

Wata sanarwa da kakakin fadar gwamnatin Najeriya Femi Adesina ya fitar a yau Asabar, ta ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aiki da sakon gaisuwa da jinjina ga Ikenna Nweke, wanda har ila yau, ya ki karbar tukwici daga hannun hukumomin kasar bayan da aka yi masa tayi.

Sanarwar ba ta ambaci adadin kudaden da Nweke ya tsinta ba, amma ta ce "makudan kudade ne a cikin 'yar jakar kudi da ake sakawa a aljihu."

"Shugaba Buhari na yin jinjina ga Nweke, saboda hali na gaskiya, sanin ya kamata da wadatar zuci da ya nuna." Sanarwar ta Adesina ta bayyana.

Kakakin fadar gwamnatin Najeriya ya kara da cewa, "halaye na gari dabi'a ce da aka san 'dan Najeriya da su, ba aikata miyagun ayyuka ba."

Nweke dalibi ne a Jami'ar Tsukuba da ke kasar ta Japan, wanda har ila yau ya ke karantarwa.

"Lallai ka nunawa duniya cewa 'yan Najeriya suna da kyawawan halaye na koyi." Wasikar da aka aikawa Nweke wacce daya daga cikin hadiman fadar shugaban Najeriya Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Asabar ta ce.

Wannan al'amari na faruwa ne a daidai lokacin da rahotanni da dama ke nuna yadda ake zargin 'yan Najeriyar da aikata ayyukan damfara musamman a kasashen waje.

A 'yan kwanakin nan 'yan sandan kasa da kasa suka kama Ramon Olorunwa Abbas da aka fi sani da "Hushpuppi" a Dubai inda ake zargin shi da aikata ayyukan damfara a kasashe daban daban ciki har da Amurka.

A jiya Juma'a aka gurfanar da Hushpuppi a wata kotu da ke Chicago a Amurkar bayan da aka mika shi ga hukumomin kasar.

"Wannan hali da Nweke ya nuna, ya zo a daidai gabar da Najeriya ke bukatar ta nuna asalin kyawawan halayen 'yan kasarta." Sanarwar ta Adesina ta ce.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG