Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 18 A Afghanistan


An kaiwa wani ayarin Sojojin kasar Afghanistan harin kunar bakin wake

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari akan wani ayarin sojan kasar Afghanistan, har ya hallaka 18 daga cikinsu, ya raunana wasu shidda.

Jamiai sunce wannan harin na yau Assabar an kai shi ne a lardin Khost dake gabascin kasar inda aka auna wata bataliyar soja ta musamman dake bada kariya ga sojan Amurka dake yankin.

Kakakin ma’aikatar tsaron Afghanistan, Najib Danish yace dan kunar bakin waken ya shake motarsa da nakiyoyi ne sannan yaje ya rabka ta akan ayarin motocin wadanan sojojin kusa da wata tashar mota wacce galibin mutanen dake wurin duk fararen hula ne.

Tuni dai kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG