Daliban jami’ar NIGER-DELTA da ke tsibirin Wilberforce a jihar Bayelsa da ke yankin Kudancin Najeriya sun ta da bore domin nuna kin amincewarsu da wata sabuwar dokar hukumar makarantar na tilastawa dalibai sanya kayan makaranta.
Daliban sun fara zanga-zangar ne bayan da shugaban makarantar Samuel Edoumiekumo ya ziyarci tsangayar ilimin Injiniyanci, domin bayyana matakin amfani da kayyan makaranta da kuma bayyana rufe kafar biyan kudin makaranta ta yanar gizo na shekarar 2020/2021.
Edoumiekumo ya bayyana cewar wannan sabuwar dokar sanya kayan makarantar ta biyo ne bayan wata ganawa da hukumomin jami'ar suka yi bayan wani harbe-harben da aka yi a kwanakin baya wanda ya kai ga harbe wani dalibi a ka.
Ya kuma nisanta kansa daga wannan al’amari tare da jaddada cewa tun a shekarar 2017 ne hukumomin suka fara tattaunawa a game da daukar wannan matakin, a lokacin da shugabannin tsangayun jami’ar suka kawo wannan shawarar a matsayin hanya daya tilo da za'a iya tantance daliban makarntar daga bata gari.
Sanya kayan makaranta a jami’o’in Najeriya ba abu ne saban ba, ko da yake a can baya, a samu labarin yunkurin wasu jami’o’i masu zaman kansu da suka yi kokarin tilastawa dalibansu sanya kayan makaranta domin tabbatar da cewa dalibai suna sanya sutura mai mutumci.