Zanga-zangar nasu nada nasaba da jinkirin turasu asibitin koyaswa kamar yadda karatun likita yake a sauran jami'o'in kasar ta Najeriya.
Daliban sun toshe kofar shiga jami'ar dauke da kwalaye suna neman 'yanci. Sun dauki dogon lokaci suna tsaye a kofar.
Daga bisani sun wakilta daya daga cikinsu yayi jawabi a madadinsu ba tare da bayyana sunansa ba domin karin haske akan abun da ya tunzurasu suka shiga zanga-zangar. Wakilin nasu yace matsalarsu ita ce suna neman hukumar dake kula da ilimin likita ta zo ta tantancesu domin idan bata yi ba babu inda zasu. Yace an dade ana cewa za'a yi yau za'a yi gobe.
Karatun likita shekara shida ake yi kafin a gama. Shekaru uku na farko ana yinsu ne cikin dakunan karatu. Bayan an gama sai kuma dalibai su yi shekara uku a asibitin koyaswa. Matsalar yanzu ita ce asibitin da zasu yi anfani dashi ba'a gama aikinsa ba kuma hukumar tantancewa bata zo ta gansu ba. Wasu sun kai shekara biyar har yanzu suna wuri daya, basu wuce matakin karatu na uku ba.
Akan wai gwamna ya debi wasu ya turasu waje, wakilinsu yace mutane 20 ne kawai cikin su fiye da 200. Wadanda aka aika waje da suna jami'ar ne da suna cikin shekara ta shida ke nan. Su ma din da aka kaisu waje shekara uku da rabi zasu kara yi.
Amma su basa son a kaisu koina a dai karasa masu asibitinsu su cigaba. A sa kayan aiki su yi aikin. Yace duk jami'ar babu wanda yake biyan irin kudin makarantar da suke biya. Iyayensu na fama dasu. Su ne suke basu kudi suke kuma kula dasu. Inji wakilin wai shugabannin jami'ar suna wasan kwallon kafa dasu. Amma sun gaji da hakan.
Farfasa William Kurit mataimakin shugaban jami'ar yace gwamnati na kokari matuka akan bukatun daliban. Yace daliban sun yi zanga-zangar ne cikin rashin sanin abun da ake yi. Misali, cikin 'yan kwanakin da suka wuce gwamnati ta samar da kudade kuma an gama wasu ayyuka da aka fara yi. Abubuwan da suka rage a kammala asibitin basu da yawa. Ba da dadewa ba za'a bude asibitin. Ita ma jami'ar ta tanadi kudaden da za'a sayo manya manyan kayan aikin da babu irinsu a Kaduna.
An yi zanga-zangar ne cikin cikakken tsaro. Kwamishanan 'yansandan jihar Mr Shehu Usman Umar yana wurin kuma yace sun zo wurin ne su tabbatar wani mugun abu bai faru ba. Yace aikinsu ne idan irin wannan ya faru su zo su kare lafiya. Ba zasu tabasu ba sai dai idan sun fara taba motocin mutane ko mutane.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara.