Daliban sun gudanar da taron gangami kwanaki biyu Kenan na yunkurin tayar da tarzomar daliban yaci tura saboda yawan jamian tsaron da aka jibge a kofar jamiaar ta Yamai.
Daliban dai sun nuna damuwa ne akan wasu matsaloli da dama ciki ko har da rashin biyan su alawus-alawus inji Ibrahim Bubakar mataimakin sakaren kungiyar daliban.
‘’Ga zancen da nake muku zuwa wannan ranar da muke ciki batun alawius-alawus din mu gwamnati tana masa rikon sakainar kashi,domin kawo yanzu ba biya mu shi ba.Kuma dalilin da ake bamu shine cewa wai kasa bata da kudi, mu ana muna gafara sa ne amma bamu ga kagho ba”.
Sai dai kuma a waje daya da wakilin sashen Hausa Sule Mummuni Barma ya tuntunbi darekta mai kula da biyan wadannan kudaden Mallam Alasan Abubakar Gawo yace wannan batu na dalibai akwai rudani a cikin sa, ga dai abinda ya shaidawa Sule din.
‘’Jiya da karfe 6 na yamma muka rabu cewa ga yadda za a yi domin biyan wadannan kudaden.’’
Ga Sule Mummuni Barni da ci gaban Rahoton 2'40