Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Ukraine da 'Yan Tawaye Suna Cigaba da Gwabza Fada


Filin saukar jirgin sama dake Danetsk inda ake gwabza yaki
Filin saukar jirgin sama dake Danetsk inda ake gwabza yaki

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma dakarun Ukraine da na 'yan tawaye sun ci gaba da gwabza fada

Kwarya-kwaryar tsagaita wutar da aka yi ta zama suna kawai a tashar jirgin saman Donetsk dake gabashin Ukraine, inda aka yi kazamin fada jiya tsakanin dakarun Ukraine da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rasha.

An ji karar makaman Igwa a sararin sama, yayinda rundunar sojin Ukraine take zargin ‘yan tawayen da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da nufin kawo karshen rikicin da ya yi sanadin kashe sama da mutane dubu uku da dari biyar tun daga watan Afrilu.Ukraine tace an kashe sojojinta biyu a fadan na baya bayan nan, aka kuma jiwa wadansu shida rauni cikin sa’oi 24 da suka shige. ‘Yan awaren kuma sun ce an kashe mayakansu uku, talatin da biyu kuma suka ji rauni.

Ukraine da ‘yan tawayen suna daukar tashar jirgin saman ta Donestsk a matsayin wani wuri mai muhimmanci a yunkurinsu na kwace ikon yankin. An kuma ci gaba da musayar wuta a wurin duk da yarjejeniyar tsaigaita wutar da aka cimma wadda kuma tana aiki a galibin yankunan gabashin Ukraine.

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta bukaci dakarun kasar Ukrain da kuma ‘yan tawayen su janye daga bakin daga su kuma kayyade wani wuri mai tazarar kilomita talatin da zai kasance tudun-mun-tsira. Sai dai Ulraine tace ba zata janye ba sai ‘yan tawaye sun daina harbi daga wurinda suka ja daga, da ya hada da tashar jirgin saman, yayinda ‘yan tawayen kuma basu nuna sha’awar janyewa daga muhimman gine ginen da ke karkashin ikonsu ba kusa da wurin da ake hada hadar sufuri.

An ci gaba da musayar wuta kusa da tashar jirgin saman a cikin ‘yan kwanakin nan, abinda ya shafi gine ginen gidajen kwana da wata makaranta da tashar motocin safa da kuma wani ofishin kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross.

XS
SM
MD
LG