Sudan ta ce ta kai harin daukar fansa akan wani muhimmin gari na wani yanki mai arzikin man fetur, da dakarun Sudan ta Kudu su ka mamaye a farkon wannan satin.
Kakakin rundunar sojojin Sawarmi Khaled Saad ya fadi jiya Jumma’a cewa dakarun Sudan sun danna zuwa garin Heglig.
Fadar Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ta ce Sudan ta Kudu za ta janye daga Heglig idan aka samar da tartibin tsarin da zai tabbatar da cewa Sudan ba ta yi amfani da wurin wajen kai hari wa Kudu ba.
Fadar ta ce ana iya girke dakarun shiga tsakani har sai Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma maslaha kan takaddamar wuri mai arzikin man fetur.
Sakatare Janar na Kungiyar ‘Yanto Kudancin Sudan (SPLM, a takaice) Pagan Amum na son MDD ta girke dakarun tabbatar da zaman lafiya a wurin ta kuma bullo da tsarin sa ido don tabbatar da cewa kowane bangaren na kiyaye yarjajjeniyar zaman lafiyar.
Amun ya koka cewa Sudan na kai hare-hare barkatai kan fararen hula, amman ba za ta iya yakin ba.
Dakarun Sudan ta Kudu sun kwace iko da garin Heglig ranar Talata, wanda hakan ya janyo zargin takalar fada daga Arewa.
Ministan Tsaron Sudan ta Kudu ya fadi jiya Jumma’a cewa dukkannin bangarorin biyu na tura karin dakaru zuwa fagen daga bayan sun yi sati guda su na ta tashin hankali da zaman dardar.