Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Soja Sun Damke Mutumin Dake Yiwa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Taraba


Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Hakan na kunshe n a cikin sanarwar da mai rikon mukamin mataimakin daraktan hulda da jama’a ma burged ta 6, Kyaftin Olubodunde Oni, ya rabawa manema labarai.

Dakarun rundunar sojin Najeriya na “Operation Whirl Stroke” sun kama wasu mutane 3 da suke zargin ‘yan bindiga ne tare da wani mai safaran makamai dake da alaka da ‘yan ta’adda a ciki da wajen jihar Taraba.

An samu nasarar ne sakamakon samun sahihan bayanan sirri, inda aka kaddamar da wani samame na musamman a ranar 7 ga watan Oktoban da muke ciki a yankin Andemin na karamar hukumar Karim Lamido.

Bayanan sun kuma taimaka wajen kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a kauyen jeb-jeb, dake kan iyakar jihohin taraba da filato.

Hakan na kunshe n a cikin sanarwar da mai rikon mukamin mataimakin daraktan hulda da jama’a ma burged ta 6, Kyaftin Olubodunde Oni, ya rabawa manema labarai.

An hakikance cewar ‘yan bindigar da aka bayyana sunayensu da adamu abubakar da muhammad bello da musa adamu nada hannu a jerin laifuffukan da aka aikata a yankin, ciki harda fashi da makami da satar mutane da kaiwa kauyuka munanan hare-hare.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG