Sakamkon harin da aka kai a birnin Paris, jiya Litinin Amurka ta soke shirinta na kyale mutane daga kasasahe 38 a fadin duniya, su shiga kasar ba tareda VISA ba. Yanzu ta dauki karin matakai na tantance mutanen da suke da nufin zuwa Amurkan.
Fadar White House tace hukumar kare cikin gida da ake kira Homeland Security, ta sauya shirin shigowa babu VISAr. Yanzu zata tanatance ko masu sha'awar zuwa kasar sun ziyarci kasashe da Amurka take kallo a "zaman mafakar 'yan ta'adda."
Bugu da kari hukumomi a Washington suka ce suna tunanin fara aiki da wani shiri na gwaji, na daukar bayanan masu shigowa Amurka, da zasu hada harda daukar hoton yatsu,karkashin shirin, kamin a kyale matafiyan su shigo cikin kasar.
Duk shekara akalla mutane milyan 20 ne suke shigowa nan Amurka daga kasashe 38 da Amurka take aiki tareda su karkashin wannan shirin.