Wani shararren dan damfara da ke zaman gidan kaso, ya saci dala miliyan daya, kwatankwacin naira miliyan 360 duk da cewa yana tsare.
Olusegun Aroke, wanda aka yanke hukuncin shekaru 24 a gidan maza na Kirikiri da ke jihar Legas a kudancin Najeriya, ya aikata damfarar ne daga dakinsa ta hanyar amfani da yanar gizo.
Matashin ya aika zunzurutun kudade daga asusun bankinsa zuwa wani asusu bayan da ya samu taimakon wasu wajen samun kafar yanar gizo da kwamfuta don yin wannan aika-aika.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, ta bayyana cewar ta samu bayanan sirri dangane da yadda Aroke ke gudanar da ayyukansa na damfara.
A cewar mai bincike na musamman, Aroke ya samu yanar gizo a wayarsa ta hannu wanda ya yi amfani da ita wajen aika kudaden.
Ya kara da cewar matashin ya bude asusun bankuna guda biyu da sunayen karya da suka hada da Akinwunmi Sorinmade, kana ya sayi motoci da gidajen alfarma duk yana gidan yarin.
Bayanai sun yi nuni da cewa, duk da yana zaune a gidan kaso, Aroke kan yi amfani da asusun bankin matarsa wajen aikawa da karbar kudade a kowane lokaci, kamar yadda jaridar yanar gizo ta Daily Mail.com ta ruwaito, wacce itama ta samo labarin daga BBC.
Tun a shekarar 2012 ake tsare da Aroke, wanda dalibi ne da ke zaune a kasar Malaysia, yana kuma shugabantar wata kungiyar masu zamba cikin aminci ta yanar gizo.
Kirikiri, na daga cikin gidajen yari mafiya tsaro a Najeriya, sannan mafi aksarin fursunoninsa wadanda suka aikata manyan laifuka ne.
Facebook Forum