Jami’an Gwamnati a Nigeria sun bayyana cewa wani lokaci cikin wan nan shekarar ce Majalisar dokokin Nigeria zata amince da sabuwar dokar hana kamfanonin mai a Nigeria kona iskar gas dake gurbata yanayi kuma yana illa ga lafiyar Bil Adama.
‘Yan Nigeria mazauna yankin Niger Delta sune suka fi cutuwa, don haka suka gabatar da kukansu ga wakilansu a majalisar dokoki. Wata matsalar kuma itace yadda ake yawaita fasa bututun mai domin satar mai wanda hakan ke gurbata kasar noma.
Felix Faei, jagoran daya daga kabilun yanmin Niger Delta ne inda suka fi bada karfi wajen sana’a kamun kifi. Yyai Karin bayani game da wannan matsala.
Yace a kowace rana ta Allah sararin samaniyar yankin nasu yana turnukewa da gurbataccen hayakin da kamfanonin mai ke fitarwa a lokacin da suke binciken rijiyar mai, sannan kuma suna gurbata ruwan yankin da suke aiki.