Siyasa a yanzu ta koma hannun matasa domin kuwa sun farka. Ganin yadda gwamnatin Najeriya ta sanya hannu akan kudurin dokar 'Not Too Young to Run. Yana daya daga cikin dalilan da matasa suka yarda da hakan, kamar yadda matashi Yuguda Abdulaziz Kabir shugaban kungiyar "One 2 Tell 10 Buhari Support Group' ke fadi.
Yuguda ya kara da cewa, a wannan gwamnatin, an samu dan canji kadan, sabanin gwamnatocin da suka gabata, duk kuwa da cewa har kawo yanzu matasan basu samu yadda suke soba, misali, an samawa matasa ayyukan yi.
Ire-iren su harkar noma da bangaren ilimi kamar shirin nan na N-power, wani yunkuri ne na samawa matasa aikin yi. Ya kara da cewa yanzu a wani dan kwaryakwaryar bincike da kungiyar 'One 2 tell 10 Buhari support group' tayi matasa sun fito domin a dama da su.
Kimanin kashi 40 cikin dari ne suka fito daga cikin matasa ake kuma damawa da su a harkokin siyasa a yanzu, kaso mai tsoka ne suka fito, su ma domin su tsaya wasu takarkaru kamar yadda saura manyan 'yan siyasa ke yi.
A yawon fadakarwar da suke yi suna kokarin jaddadawa matasa kwarin gwiwa, cewar su fito sannan su ajiye siyasar kudi domin samawa kasa madafa, wannan dabi’ar kuwa ta shaye shayen kwaya, saura dan lokaci kadan ragowar matasan su farga su daina, sakamakon tasirin fadakarwa da suke yi wa 'yan uwansu matasa.
Facebook Forum