'Yan sanda kasar Faransa sunce an dan dakatar da yunkurin ganowa da ake yi a inda jirgin saman kasar Jamus ya fadi.
Hukumomi sunce sun gano akwatunan dauka da tattara bayanan jirgin da ake cewa black box turanci, da kuma gawarwarkin mutane. A ranar ashirin da hudu ga watan jiya na Maris jirgin saman fasinjan na kasar Jamus ya fadi a yankin tsanukan kasar Faransa ya kashe dukkan mutane dari da hamsin, wadanda suke cikin jirgin.
Masu bincike sunce bayanan da suka samu daga akwatin farko, jim kadan bayan faduwar jirgin, yasa masu bincike yanke shawarar cewa daya matukin jirgin dan shekara shirin da bakwai da haihuwa mai suna Andreas Lubitz da gangan yayi hatsari da jirgin.
Domin kuwa shi Andreas Lubitz ya kule kofan shiga inda direbobin jirgin ke zama da ake cewa cock pit da turanci, ya hana matukin jirgin mai suna Patrick Sondheimer shiga, sai ya karkata akalar jirgin da gangan, ya doshi tsanuka, inda jirgin yaje ya fadi a gefen tsaunuka. Masu bincike sunce Andreas Lubitz yayi kunnen uwar shegu da bukatar da matukin jirgin yayi ta yi masa cewa ya bude kofar. Kuma aji wadannan maganganun ne a cikin akwatin dauka da kuma tara bayanan abubuwan da suke faruwa a cikin jirgin.
A lokacinda Andreas Lubitz yake makaranta koyon tukin jirgin sama na kamfanin Lufthansa, a shekara ta dubu biyu da tara, ya fadawa makarantar cewa yana fama da matsalar damuwa sosai. To amma duk da haka kamfanin Lufthansa ya ayyana cewa ya cancanci ya tuka jirgin sama.
'Yan sanda kasar Faransa sunce an dan dakatar da yunkurin ganowa da ake yi a inda jirgin saman kasar Jamus ya fadi.