WASHINGTON —
Garin Tsagem ya shahara sosai kuma gari ne na Fulani da Malamai. Basaraken garin Buhari Usman, ya ce garin ya shahara a fannin kiwo da noma kuma har yanzu kaburburan sarakunan garin na baya na nan a wurin Dutsen Gandu.
Duk da shahararsa, garin na fuskantar kalubalen karancin samun ci gaba, musamman ta bangaren hanyoyi da kuma karancin ruwa.
Saurari cikakken shirin wanda Abdul Jani ya gabatar.