WASHINGTON, DC - Garin Farakwai dai gari ne mai tsohon tarihi da aka kafa kafin Zangon Aya da Yalwa, a cewar Basaraken garin Muhammad Labaran.
Basaraken ya ce kabilar Gbagyi ce ta fara kafa garin Farakwai, bayan da suka yi kaura kuma sai kabilar Jaba ta yi sarautar ngarin zuwa wani lokaci.
A shekarar 1888 Fulani suka karbi sarautar garin Farakwai, wato shekarun da Umaru Dan-Aliyu ya karbi sarautar, a cewar Labaran.
Noma, kiwo da saka su ne sana’oiin da aka san garin Farakwai da shi.
Saurari cikakken shirin da Nasiru Yakubu Birnin Yero ya gabatar.