‘Yan wasan kwallon kwando na Najeriya wato D'Tigers', zasu fafata da kasar Ivory Coast, domin samun tikitin shiga gasar Olumpic wanda za’ayi a shekarar 2020, za a fara buga wasan ne a yau a Guangzhou.
Bayan rashin nasara da ta yi akan kasashen Rasha da Argentina, a jiya laraba D'Tigers ta sake dawowa inda ta lashe wasan da suka buga Korea Republic da ci 108-66. Inda ta suka samu kyakkyawan matsayi na karawa da kasar Tokyo, domin samun damar shiga gasar Olumpic a shekarar 2020.
Shugaban masu horar da 'yan wasa, Alex Nwora ya ce, zasu samu samaun nasara akan Korea, Najeriya na saran za ta fafata da da 'yan kasar Ivori Coast domin tabbatar da dama fiye da abokiyar takararta, Tunisia wacce za ta hadu da Philippines a zagaye na biyu.
Tunisia da Senega da Angola da kuma Cote d’Ivoire dukkansu suna matukar son samun tikitin wasannin na Olympics. Don haka dole ne mu zage damshe domin samun damar cin gasar."
Idan DTigers za su samu nasarar samun tikitin shiga wasan gasar ta Tokyo a shekarar 2020 ba tare da wata tangarda ba, dole ne su ci wasan su da Côte d'Ivoire, domin su karbi bakuncin China, inda zasu zama babbar kungiyar a Afirka da ke kan gaba a China.
A halin yanzu, suna da bambanci mafi girma na maki +24 daga cikin kasashen Afirka a gasar cin kofin duniya na FIFA, wanda ake gudanarwa.
Facebook Forum