A Litinin din data gabata ne rahotan bullar wata cuta ya bayyana wadda tun a lokacin ta hallaka mutane 8, kuma ya zuwa Larabar nan alkaluman wadanda suka mutu ya kai 11.
Dayake tabbatar da al’amarin ga manema labarai jiya da marece kwamishin lafiya na Kano Dr Kabiru Ibrahim Getso ya ce bayan gudanar da binciken kimiyya, ayarin jami’an lafiya daga ma’aikatar sun tabbatar da cewa, cutar sankarau ce ta hallaka mutanen kuma yanzu haka akwai wasu mutane 6 da suka kamu da ita.
Kwamishanan ya kara da yin bayani akan cutar wadda ya ce tana yaduwa ne cikin mutane. Cutar na kawo kumburin dake rufe kwakwalwa. Alamomin cutar sun hada da zazzabi mai zafi, ciwon kai mai tsanani, tashin zuciya, amai da sankarewar wuya
Yanzu haka dai wasu majiyoyi na cewa, adadin wadanda suka mutun ka iya haura 11,la’akari da cewa, akwai wadanda annobar ta ritsa dasu ba tare da gwamnati ta san dasu ba.
Amma kwamishinan lafiyar na Kano yace yanzu haka sun fara daukar matakai game da wannan annoba. Matakan sun hada da bibiyar mutane ana bincikarsu domin gano masu dauke da kwayar cutar. Sannan an samar da ma’aikatan gaggawa domin kai doki duk inda aka ji labarin alamar bullar cutar domin a yi bincike a san abun dake faruwa. Kazalika, gwamnatin jihar ta sayi magunguna ta ajiye a asibitoci daban daban musamman a wuraren da cutar ta bulla. An kuma dauki matakin wayar da kawunan mutane akan cutar
Wannan cuta ta sankarau dai ta kashe kimanin mutane 100 cikin kasa da watanni biyu a jihohin Jigawa da Katsina masu makwaftaka da jihar Kano
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Facebook Forum