Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Sankarar Nono Bata Kisa Muddin Anyi Gwaji Da Wuri: Wata Kungiyar Jin Kai A Kamaru


Mata a asibiti
Mata a asibiti

Wani ayarin masu gudanar da aiyukan jin kai a Kamaru ya kai ziyara gida gida a yankunan dake cikin kauyuka, domin bikin watan wayar da kai, kan cutar kansar mama, ko sankarar nono, inda suke ba mata shawara da su ziyarci asibitoci domin ayi musu gwaji kyauta, a kuma basu magani.

Kimanin kashi 60% daga cikin 100 daga cikin sama da mata 7000 da aka samu dauke da cutar kansar mama a Kamaru sun mutu har lahira a bana, saboda rashin zuwa asibiti a kan lokaci, cewar jami’ai.

Wata daliba a fannin ilmin tarihi mai shekaru 30, Emilie Nadege Atangana, ta shaidawa wani gungun mata da yammata a jami’ar Yaounde, yadda ta shiga mummunan tashin hankali a lokacin da aka gano cewa, tana dauke da cutar kansar mama.

Tace, da dama daga cikin yan’uwanta, abokai da abokan karatun ta, sun juya mata baya tare da debe tsammanin cewa ba zata yi wani tsawon rai ba. tunda suka ji labarin cewa an gano tana da kansar nono a watan Yuli na shekarar 2020.

Atangana tace ta fara samun karfin guiwar samun magani ne lokacin da likitocin cututtukan mata da na sauran cututtuka, na asibitin Yaounde su ka shaida mata cewa kashi casa’in daga cikin dari na sabon kamuwa da cutar kansar mama na iya warkewa sarai.

Jami’an gwamnatin Kamaru da kungiyoyin jin kai sunce an tura mutanen da suka warke daga cutar kansar nono, irin Atangana zuwa kauyuka da garuruwa a matsayin wani bangare na bikin watan wayar da kan mata game da cutar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace, an kebe watan Oktoba a matsayin watan wayar da kan mata dangane da cutar ta sankarar nono ‘Pink Month’ domin sanar da mutane ilmi game da cutar, da ya hada da yadda za’a gane cutar tun da wuri da alamomin ta.

Ita ma Mesoke Ngwese Agbaw mai shekaru 42 a duniya da ta warke daga cutar sankarar nono, tana ilmantar da mutane domin su san cewa, ana warkewa daga cutar muddin aka gano ta da wuri. Tace bai kamata mutane su rika boye masu cutar a gida ba, a karshe har su mutu da tunanin cewa, ba’a warkewa daga cutar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG