Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Coronavirus Ta Hallaka Wasu 'Yan Najeriya a Amurka


Yayin da yawan masu Coronavirus ke karuwa a birnin New York, shi ma karamin ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin ya kara kaimi wurin kula da ‘yan Najeriya mazauna New York da jihohin kewaye, musamman bayan da 'yan Najeriya a Amurka suke alhinin mutuwar wasu 'yan uwansu su uku sakamakon kamuwa da cutar ta COVID 19.

Da yake zantawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Karamin Jakadan Najeriya mai jagorantar ofishin na New York Ben Okoye ya ce "lallai ana cikin wani lokaci da ba a saba gani ba kuma ba a iya fita saboda kowa na killace bare a je idan wani na da bukata."

Ya ce "abin da muke yi shine muna tuntubar wadanda suka rasa ‘yan uwansu domin jajanta musu kuma muna sanar da gwamnati a gida halin da ake ciki."

Mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 a Amurka sun kai 362,759, yayin da a jihar New York masu cutar suka haura dubu 100.

Lamarin da ke tada hankalin mazauna jihar da kewaye.

Mutuwar ‘yan Najeriya uku a Amurka sakamakon annobar Coronavirus ta ja hankalin mahukuntan kasar a kan neman hanyoyin agaza wa masu neman taimako a dai-dai wannan lokaci da kowa ya makale a gida.

Karamin ofishin jakadancin Najeriya da ke New York ya bada wata lambar da za a tuntubeshi idan bukatar hakan ta taso a cewar jakada Okoye.

Kamar yadda gwamnatin tarayya da hukumomin jihohi da na kananan hukumomi ke taimaka wa marasa galihu a wannan lokaci da dokokin hana zirga zirga ke aiki a Najeriya, shi ma karamin jakadan Najeriya mai jagorantar karamin ofishin jakadancin Najeriya a New York ya ce a shirye suke su bai wa duk wani dan Najeriya taimako.

Saurari wannan rahoton a sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG