Shahararren dan wasan kwallon kafa nan dan kasar Portugal, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya lashe kambin zakaran dan wasan kwallon kafa na Ballon D’Or, na bana.
Ya doke abokan takarar sa Lionel Messi, mai takawa Barcelona leda da Antoine Griezmann, wanda shi kuma Atletico Madrid, yake murzawa leda.
Dama a can baya Cristiano Ronaldo, ya lashe wannan kambi har sau ukku, wanna shine karo na hudu da shahararren dan wasan zai lashe wannan gagarumin kambi.
Ronaldo, dan shekaru talatin da daya a kakar wasan na bana ya fara ta da kafar dama ce inda kungiyarsa ta Atletico Madrid, ta lashe gasar lig din zakaru. Kuma ya jagoranci kungiyar kwallon kafa na kasar sa watau Portugal, inda suka lashe gasar zakarun Turai wanda aka buga a kasar Faransa.
Wadannan nasariri da ya samu sun taimakamasa wajan lashe wanna kambin na Ballon D’Or, na bana.
Har ila yau ana kuma harsashen cewa tana iya kasancewa shi zai lashe kyautar FIFA, na zakaran dan wasa na duniya.
Duk da wannan nasarar da ya samu na lashe Ballon D’Or na bana bai kama kafar Lionel Messi, ba domin shi sau biyar ya lashe Ballon D’Or.