Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal mai taka leda a Kungiyar Real Madrid Cristiano Ronaldo shine kan gaba waja zurara kwallaye a raga a gasar cin kofin zakaru na nahiyar turai wato UEFA Champions League tun kafa hukumar da akayi na UEFA a 1955 kimani shekaru 61 baya.
Kawo yanzu dai Cristiano Ronaldo, ya jefa kwallaye har tasa'in da biyar a wasannin daban daban na gasar zakarun nahiyar Turai watau champion league.
A yayin wasan Real Madrid, da Borussia Dortmund, ne Cristiano Ronaldo, ya zura kwallon sa na tasa’in da biyar a cikin minti na goma sha bakwai da fara wasan inda aka tashi wasan biyu da biyu a gidan Dortmund.
Shi kuwa takwaransa Lionel Messi na Barcelona shi yake mataki na biyu inda shima ya jefa kwallaye har tamanin da shida a gasar ta cin kofin zakaru nahiyar Turai.
WASHINGTON, DC —