A wani mataki na hana yaduwar cutar coronavirus, majalisar dattawan Najeriya ta ce daga gobe Talata 24 ga watan Maris zata dage dandalin sauraren bahasin jama'a da kuma hana baki kamar dalibai da kuma manyan baki kai wata ziyara ta musamman a majalisar.
A wata mahawarar da majalisar dattawan ta yi a game da matakin dakile yaduwar cutar coronavirus, majalisar ta kuma yaba da kokarin da gwamnati ke yi. tare da yin kira da a kara kaimi wajen daukar kwararan matakai domin kare yaduwar cutar.
A hirarshi da Sashen Hausa, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya ce sun bi sahun abinda ke faruwa ne a kasashen duniya saboda a kare lafiyar ‘yan majalisar, da ma baki masu kai ziyara tunda an hana taron jama'a a wurare da dama, kamar makarantu da wuraren taron da zai wuce mutum talatin ko hamsin.
Sai dai dan majalisar wakilai Abdullahi Salame da Sashen Hausa ya yi hira da shi, ya ce ba su samu irin wanan umurnin a bangaren su ba tukuna, sai dai yana ganin a matsayinsu na wakilan jama'a, bai kamata a ce majalisar ta dage zamanta ba tunda gwamnati ce mai daukar matakan tabbatar da kare lafiyar al'umma har ma da 'yan majalisar.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya ta ce mutum 30 ne aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 a Najeriya, yayinda mutum guda ya rasu sakamakon kamuwa da cutar.
A saurari cikakken bayani cikin sauti.