A yau Litinin Firayim Ministan Japan Shinzo Abe ya ba da sanarwar cewar, kasarsa za ta bukaci kebancewa na tsawon kwanaki 14 ga duk baki masu shigowa kasar daga Amurka, yayinda adadin masu kamuwa da cutar Coronavirus ta ke karuwa a duniya.
Bukatar kebewa ta hada da ‘yan kasar Japan da ‘yan Amurka dake zaune a kasar, wadda kuma za ta fara aiki ranar alhamis mai zuwa, har zuwa karshen watan Afrilu. Wannan matakin ya zo ne bayan da kasar Japan ta habaka shirin ta na hana ‘yan kasar zuwa Amurka, Minista Abe yayi kira ga 'yan kasar ta Japan da kar su yi tafiye-tafiye marasa amfani.
Sanarwar Abe ta zo ne a yayin wani taron da kwamatin aikinsa na gwamnatin tarayya game da barkewar cutar COVID-19, tare da yin nuni da yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a duniya.
Abe ya ce sabuwar bukatar ta zo daidai da matakan da wasu kasashe suka dauka, ciki har da Amurka, wanda ya ba da rahoton karuwar sabbin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a cikin ‘yan makonnin nan.
Alamu sun nuna Japan ta sami nasarar rage yaduwar cutar a cikin kasarta, tare da wandanda suka kamu da cutar, inda ta sami mutane 1,101 kadai da suka kamu da cutar ya zuwa yau Litinin, a cewar rahoton binciken da Cibiyar Kimiyya da fasaha ta Johns Hopkins ta hada.
Facebook Forum