Gwamnatin jihar Adamawa ta sanya dokar hana fita a fadin jihar tsawon kwanaki 14 daga daren yau Juma’a 24 ga watan Afrilu zuwa 8 ga watan May una shekarar 2020.
Gwamnatin jihar ta ce, daukar matakin a yanzu ya zama dole ganin cewa jihar ta shiga sahun jihohin da aka samu bullar kwayar cutar coronavirus mai lakabin COVID-19, ta kuma ce dokar za ta fara aiki ne daga tsakiyar daren yau Juma’a har tsawon makonni biyu.
Mr, Solomon Kumangar dake zama daraktan yada labaran gidan gwamnatin jihar, shi ya bada sanarwar a madadin gwamnatin jihar ya kuma ce akwai ma’aikata masu aiki na musamman da dokar bata shafa ba, kamar masu saida kayan abinci, jami’an kiwon lafiya, jami’an tsaro, ‘yan jarida, da sauran su.
Haka kuma gwamnatin jihar ta kafa kotun tafi da gidanka domin hukunta masu ketare doka.
Wannan na zuwa ne yayin da al’ummar Musumi ke soma azumin Ramadan inda shugabanin addini ke yin kira da a bi umarnin hukumomi tare da maida hankali wajen addu’o’in Allah ya kawo karshen wannan cuta.
Dr Hafiz Sa’id na cibiyar Haidar Centre, ya ce a wannan yanayi na COVID-19, ya kuma bukaci jama’a su zama masu tausayi da kyautata wa al’umma a wannan lokacin.
Ita ma kungiyar kristocin Najeriya ta CAN ta bi sahu wajen taya al’ummar Musulmi murnar watan azumin tare da yin kira a maida hankali wajen yin addu’o’in neman sauki daga Allah da kuma ganin karshen coronavirus.
Rabaran Stephen Dami Mamza, shine shugaban kungiyar a jihar Adamawa ya yi kira ga al’ummar musulmi da su taya Najeriya da sauran kasa baki daya addu’a yadda Ubangiji Allah zai magance wannan annobar, ya kuma kara jan hankalin jama’a akan kiyaye ka’idodin da gwamnati ta sanya don dakile yaduwar cutar coronavirus.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum