Sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata je Uganda domin tattaunawa da shugaban kasar Yoweri Museveni, yayinda take ci gaba da ziyarar kasashen nahiyar Afrika.
Clinton zata yi amfani da tattaunawar da za a yi gobe Jumma’a wajen musayar miyau a kan rawar da kasar Uganda take takawa a matsayin babbar abokiyar kawancen Amurka, a tsaron yankin, ta kuma karfafa tsarin damokaradiya da kare hakin bil’adama.
Jiya laraba Clinton ta gargadi shugabannin kasashen nahiyar Afrika da cewa, tilas ne su mutunta hakin al’ummominsu idan ba haka ba su rasa mulki.
Ta bayyana yayin jawabinta a Senegal cewa, mutanen nahiyar Afrika suna neman canji a kasashen da masu hali da shuni kalilan suke ci gaba da azurta, yayinda galibin al’ummar kasa ke fama da talauci.
Ta kuma bayyana tsare tsaren Amurka dangane da nahiyar Afrika da tace, suna la’akari da gurorin ci gaban kasa da habakar tattalin arziki, da wanzar da zaman lafiya da tsaro da kuma karfafa tsarin damokardiya.
Wannan ce ziyara ta farko da Clinton ta kai kasashen nahiyar Afirka yankin Hamada tunda shugaba Obama ya sanar da sabon tsarinshi a watan Yuni.
Ziyarar ta Clinton zata kuma kaita kasashen Sudan ta Kudu da Kenya da Malawi da kuma Afirka ta Kudu. A Afirka ta Kudu, zata gana da tsohon shugaban kasar mai rajin kare damokaradiya Nelson Mandela.