Sakatariyar harakokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta ce komi na iya faruwa a daidai lokacin da Amurka ke duba yiwuwar daukan kowane irin matakin dakatar da munmunan halin ba sani ba sabon da gwamnatin kasar Libiya ke nunawa ‘yan kasar.
Clinton ta fada a wajen wani taron manema labarai a kwamitin kula da hakkokin bil Adama na MDD a yau litinin a birnin Geneva cewa shugabancin kasar Libiya ya haramta ga Muammar Ghaddafi kuma dole ya bar mulki ba tare da wani jinkiri ba. Ta ce Amurka da abokan huldar ta na kokarin kaddamar da martanin da ya dace da balahirar kasar Libiya.
Clinton ta ce Amurka ta ware karin dola miliyan goma na taimakon gaggawa ga kungiyoyin tallafin da ke kasar Libiya,kuma nan take Amurka za ta tura tawagogi biyu na ‘yan agajin jin kai domin su agazawa mutanen da ke gudu su ka kuma yada zango akan iyakokin Libiya da Tunisia da kuma Masar.
A halin da ake ciki kuma, jami’an Tarayyar Turai da ke taro a birnin Brussels sun ce kasashen tarayyar 27 sun cimma jituwa akan wani kunshin matakan ladabtar da shugaban kasar Libiya Muammar Ghaddafi, wadanda kuma ke karfafa matakan da kwamitin sulhun MDD ya zartas a makon jiya.
Jami’an sun ce matakan ladabtarwar da Tarayyar Turai ta dauka sun hada da haramta sayen makamai, hana izinin yin balaguro ga Mr. Ghaddafi da mutanen shi, na kurkusa da shi, da kuma hana su yin amfani da kadarorin su, da ma kuma wadannan matakai na cikin kudirin da kwamitin sulhun MDD ya zartas ranar asabar.