Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Ta Nemi Hukumar FBI Ta Gayawa Duniya Duk Abunda Ta Bankado


'Yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton
'Yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton

Hakan ya biyo bayan sanarwar da hukumar ta bayar cewa ta gano wasu karin emails masu nasaba da bincike da gudanar.

'Yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton, ta yi magana kan sanarwar da hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka (FBI) tayi cewa ta gano karin email masu nasaba da binciken da ta gudanar kan Mrs Clinton, gameda amfani da asusun aikewa da sakonni na kashin kanta yayin tana sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Jiya Jumma'a Mrs Clinton ta bayyana gaban manema labarai sa'o'i bayan da darektan hukumar James Coney ya bada wannan sanarwa cewa an gano emails din ne yayin wani bincike na daban wanda hakan ka iya shafar ita Mrs. Clinton.

Mrs Clinton tayi kira ga hukumar ta bayyanwwa duniya duk bayanan da take gano, ta kara da cewa "ko shi darektan ya fada cewa sai tayu bayanan basu da wani muhimmanci.. domin haka "a fito da su duka a fili", inji Madam Clinton.

Wasu majiyoyin gwamnati sun fada jiya jumma'a cewa sun gano sabbin emails daga asusun tura sakonni na Mrs Clinton, bayan da ta kwace wasu na'urori daga wata hadimar Clintoin Huma Abedin da kuma mijinta Antony Weiner wand a tsohon dan majalisa ne.

'Yan jam'iyyar Republican sun yi murna saboda suna kallon sabbin emails da aka gano a zaman shaidar zxargi da suke yiwa Clinton yadda take amfani da bayanan gwamnati ta hanyoyi da ba'a saba ba.

XS
SM
MD
LG