Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Clinton Da Trump Na Ci gaba Da Kai Ruwa Rana


Dan takarar shugabancin Amurka, Donald Trump (Hagu) da abokiyar hamayyarsa ta Democrat Hillary Clinton (Dama)
Dan takarar shugabancin Amurka, Donald Trump (Hagu) da abokiyar hamayyarsa ta Democrat Hillary Clinton (Dama)

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican, Donald Trump, da abokiyar karawarsa Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat sun fito da kakkausar harshe suna caccakar juna, kwana guda a bayan da suka bayyana a wani zauren muhawara kan batutuwan tsaron kasar.

A lokacin da yake jawabi a wata makaranta a birnin Cleveland a Jihar Ohio, Trump ya ce irin rawar da Clinton ta taka a muhawarar ta daren laraba, ta nuna cewa ba ta cancanci zamowa shugabar Amjurka ba.

Trump ya ce har yanzu Clinton ta na ci gaba da kin daukar alhakin gurbatattun manufofinta game da yanking Gabas ta Tsakiya a lokacin da take rike da mukamin sakatariyar harkokin waje.

Ya bayyana Clinton a zaman mai dokin kai hare-haren mamayar wasu kasashe da kifar da gwamnatocinsu, abinda ya ce ya haddasa mace-mace da hasara a Libya da Iraqi da kuma Syria.

Ita kuma a nata bangaren, Clinton ta fadawa wani taro a birnin Charlotte da ke Jihar Carolina ta Arewa cewar ta girgiza da kalamin da Trump ya yi cewa shugaba Vladimir Putin na Rasha ya fi zama shugaban kwarai a kan shugaba Barack Obama.

Ta ce wannan ba wai Rashin kishi ba ne kawai, ba wai cin mutuncin wannan kujera ta shugabancin Amurka ce ko kuma mutumin da ke rike da wannan kujerar ba. Abin ban tsoro ne, kuma abu ne mai cike da hatsari.

Clinton ta yi biris da shirin Trump da ya ce na sirri ne na takalar kungiyar ISIS.

Ta ce dalilin da yasa Trump ya ce na sirri ne shine domin a zahiri ba shi da wani shirin.

XS
SM
MD
LG