Wata Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya dake yaki da cin zarafin mata a inda ake tashin hankali, ta fadi jiya Talata cewa, irin wannan tashin hankalin ya karu sosai a Sudan ta Kudu cikin wannan shekarar, kuma akwai bukatar daukar matakin kare yawan yin fyade.
“A shekarar 2018, an sami yawaitar batutuwan da suka shafi cin zarafin mata a yankunan dake fama da tashin hankali,” a cewar Pramilia Patten lokacin da take fadawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta hoton bidiyo daga Landon. “Yawan mutanen da lamarin ya shafa a 2018 sun kai 1,157 wanda hakan ke zama mafi yawa da aka taba samu cikin shekaru uku da suka gabata.”
Pattern, wadda ke zama wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan cin zarafin mata a yankunan da ke fama da tashin hankali, ta ce cin zarafin mata a Sudan ta Kudu ya zama ruwan dare, kuma ana yi ne domin cin zarafin matan da kuma bangaren da suka fito, yawanci kabila ko jam’iyyar siyasar da suke.
An bayyana masu irin wannan cin zarafin a matsayin sojojin gwamnati da mayakan ‘yan aware.
Facebook Forum