Dogarawan sun fada a cikin wata sanarwa cewa sun kwace jirgin ruwan ne a ranar Laraba a kusa da tsibirin Farsi, arewa ga mashigar ruwan Hormuz.
Kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA ya rawaito Dogarawan tsaron su na cewa jirgin yana dauke ne da lita dubu dari bakwai na man Iran da aka yi fasakwabrin sa aka bai wa jirgin, kuma za kai a kasashen Larabawa da ke kan yankin Gulf.
Rahotannin kwace jirgin ba su nuna dalilin da ya sa za a kai man Iran zuwa kasashen Larabawan da su ma ke samar da mai a yankin tekun Fasha ba. Amma Iran din ta nuna damuwa a kan fasakwabrin man a wannan lokaci da Amurka ta kakaba ma ta takunkuman tattalin arziki da zummar takaita mata cinikin mai.
Kafafen yada labarai a Iran sun fada a watan da ya gabata cewa ‘yan fasakwabri sun sulale da litoci miliyan takwas na man da gwamnati ke sassauta farashinsa a kowace rana zuwa kasashen da farashin man ke tsada.
Facebook Forum